ABNA24 : Wannan bayyanin ya fito ne yayin wata zantawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, da takwaransa na Japan, Sem Motegi, a ranar Laraba.
Yayin tattaunawar bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin dama kasa da kasa, da kuma batun yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.
Mista Zarif, ya nanata cewa Iran a shirye take ta kawo karshen matakan da take dauka game da yarjejeniyar da zarar Amurka ta dage mata takunkuman zalunci data kakaba mata, su kuma sauren bangarorin suka cika nasu alkawura.
Iran, ta bakin ministan harkokin wajenta ta ce har kulun tana neman hanyoyon kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a rikice rikice da suka shafi kasa da kasa, ciki har da baiwa MDD, kyakyawan goyan bayan ta wajen warware rikicin kasar Yemen.
342/